Akalla Mutane 40 Sun Rasu Sakamakon Hatsarin Jirgin Kasa A Iran


4bkbd7249feab6i7jv_800c450

 

Akalla mutane 36 sun rasa rayukansu kana wasu kusan 100 sun sami raunuka sakamakon hatsarin da wasu jiragen kasa guda biyu suka yi a wata tashar jiragen kasa da ke kusa da ke garin Shahroud na lardin Semnan da ke arewa masu tsakiya na kasar Iran.

Rahotanni sun jiyo jami’an jihar suna fadin cewa hatsarin dai ya faru ne a tashar jirgin kasa na Haf-Khan da ke kusa da garin Shahroud da misalin karfe 7:40 na safiyar yau lokacin da wasu jiragen kasa guda biyu suka ci karo da junansu a tashar jirgin.

Shugaban hukumar agajin gaggawa na lardin Pir Hossein Kolivand ya bayyana cewar alal akalla mutanen 36 sun rasa rayukansu kana wasu da dama kuma sun sami raunuka. Wasu rahotannin sun ce akwai yiyuwar adadin wadanda suka rasu ya karu sakamakon munin raunin da wasu suka samu sakamakon hatsarin; kamar yadda wasu kafafen watsa labaran suka jiyo wani jami’in hukumar agaji ta Red Crescent ta jihar ta Semnan yana fadin cewa adadin wadanda suka rasa rayukan na su ma ya kai mutane 40 sannan wasu kimanin 100 kuma sun sami raunuka.

Tuni dai aka tura jirage masu saukan ungulu da motocin daukan marasa lafiya don ci gaba da ba da agaji ga wadanda hatsarin ya ritsa da su musamman bisa la’akari da gagarumar gobarar da ta tashi bayan da jiragen biyu suka ci karo da junansu..

Tuni dai aka fara gudanar da bincike don gano musabbabin wannan hatsarin wanda ya faru lokacin da wani jirgin da ke tafiya ya ci karo da wani jirgin da ke tsaye a tashar jirgin kasar.

You may also like