Akalla Sojojin Mali 5 Ne Suka Rasa Rayukansu Sakamakon Tashin Wasu Bama-Bamai


4bkc332ad9e263ivf4_800C450

Sojojin kasar Mali 5 ne suka rasa rayukansu biyo bayan tashin wasu bama-bamai masu karfin gaske, a lokacin da suke rangadi a wani yanki da ke tsakiyar kasar.

Jaridar Le Figaro ta kasar Faransa ta bayar da rahoton cewa, an tayar da bama-baman ne a yankunan Segou da kuma Mpti da ke tsakiyar kasar ta Mali, a lokacin da sojojin kasar suke gudanar da rangadi, a nan take dai sojojin 5 ne suka rasa rayukansu, kamar yadda majiyoyi a maikatar tsaron kasar suka tabbatar.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar da wannan hari, amma mahukunta  akasar ta Mali sun dora alhakin hakan a kan kungiyoyi masu da’awar jihadi.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like