Akalla ‘Yan Shiya 12 ne Da Dan Sanda daya suka Mutu A A karon Battar data gudana A Garin a Kano


Akalla mutane sha biyu ne aka kashe lokacin da ‘yan sanda suka yi arangama da ‘yan Shi’a a wajen birnin Kano, yayin da aka jikkata ‘yan sanda biyar, inda kuma dan sanda daya ya rasa ransa.

Jami’an tsaro sun ce daya daga cikin ‘yan sandan na nan rai a hannun Allah.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wani mutum yana cewa ya ga gawarwakin mutum goma.

Wani dan jarida da ke tafiya da ‘yan Shi’ar ya shaida wa majiyarmu ta BBC cewa ‘yan sanda sun harbi mabiyansu da dama, kuma akwai fargabar an kashe mutane da yawa.
Wani ganau ya shaida wa majiyarmu cewa ya ga motocin ‘yan sanda dauke da mutane hudu da harin ya shafa, amma ba tabbas ko sun mutu ko suna raye ba.

Akalla mabiya Shi’a 349 aka kashe a watan Disamban bara lokacin wata arangama da suka yi da sojoji a garin Zaria.
Wani dan ‘yan Shi’a da ya samu rauni.

‘Yan sanda sun tabbatar da rikicin na baya-bayan nan, amma kakakinsu a jihar Kano Magaji Majiya ya ce har yanzu suna tattar bayanai.
Sai dai wani jami’i da bai yarda a bayyana sunansa ba ya ce sun bude wuta ne saboda ‘yan Shi’ar sun kai musu hari. Ya kuma kara da cewa ana ci gaba da bata-kashin.
Yanzu haka an toshe babbar hanyar shiga garin Kano daga kudu, da kuma fita zuwa birnin tarayya Abuja saboda rikicin.
Mabiya Shi’ar na yin tattakin da suka saba yi ne a duk shekara zuwa garin Zaria, mai nisan kilomita 165, inda nan ne cibiyar kungiyar ta su.

You may also like