Akande da Tinubu sun gana da Buhari


Bola Tinubu jagoran jam’iyar APC da kuma Bisi Akande tsohon shugaban riƙon na jam’iyar sun gana da shugaban ƙasa Muhammad Buhari.

Duka jagororin jam’iyar biyu sun isa fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 3:50 inda kuma suka fice daga ɓangaren gidan shugaban ƙasa da misalin karfe 4:50 gidan da anan ganawar ta gudana.

Ba a bawa masu ɗauko rahoto daga fadar shugaban kasa ba damar isa wurin da jagororin suke.

Ba za a iya tantancewa ba ko ganawar tasu ta mai da hankali ne kan takarar shugaban kasa Buhari a shekarar 2019.Akande da Tinubu basu halarci taron masu ruwa da tsaki na jam’iyar APC da shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya kira ba a makon da ya wuce.

 Dukkannin mutanen biyu sun taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar Buhari a zaɓen cikin gida na jam’iyar APC dama babban zaɓen ƙasa baki ɗaya.

You may also like