Akwai Alamun Shigaba Jammeh Na Gambiya Bashi Da Niyyar Mika MulkiShugabar kasar Liberian Ellen Johnson Sirleaf, wacce ta jagoranci wata tawagar shugabannin kasashen yammacin Afrika don sasanta rikicin siyasar kasar Gambia ta ce babu wata yarjejejeniya da suka cimma don kawo karshen dambarwar.
Tun da farko dai Sojoji a Gambia sun mamaye hedikwatar hukumar zabe yayin da Jam’iyyar Mr Jammeh ta shigar da kara a kotun kolin kasar inda ta bukaci a soke zaben.
Sai dai a halin yanzu kotun bata da isassun Alkalai, saboda haka ba a san takamammen lokacin da za a saurari karar ba. Abaya dai Shugaban kungiyar ta ECOWAS, Marcel de Souza, ya yi barazanar cewa za su yi amfani da karfi idan Mista Jammeh ya ki mutunta kundin tsarin mulkin kasar.
Zababben shugaban kasar Adama Barrow, wanda ya lashe zaben na 1 ga watan Disamba, ya nemi taimakon kasashen duniya. A watan gobe ne ya kamata a rantsar da shi a kan karagar mulki.

You may also like