Akwai Kanshin Gaskiya A Rahoton Yiwuwar Fuskantar Karancin Abinci – Buhari Shugaban Kasa, Muhammad Buhari ya tabbatar da rahoton da ke nuni da cewa za a iya fuskantar karancin abinci a nahiyar Afrika inda ya roki shugabannin kasashen Nahiyar kan su bunkasa Harkokin noma a kasashen don ganin an kauce aukuwar yanayin yunwa.
Shugaba Buhari ya yi wannan ikirarin ne a yau Litinin a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wurin taron kungiyar yaki da yunwa ta RPCA wanda aka yi a Abuja inda ya nuna cewa a halin yanzu ana fuskantar karancin abinci da ake bukata na yau da kullum saboda sakaci da aka yi wajen yin watsi da harkar noman zamani.

You may also like