Akwai mago-mago a zaɓen kananan hukumomin jihar Kano -Kwankwaso


PPRabi’u Musa Kwankwaso sanata mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa ya ce zargin da ake na yara masu kananan shekaru sun kaɗa ƙuria a zaɓen ƙananan hukumomin jihar Kano ya faru ne saboda jam’iya ɗaya ce kawai ta shiga zaɓen.

Kwankwaso ya ce ba zai iya yiyuwa ba a tafka magudin zabe idan har jam’iyu masu yawa sun shiga ciki.

A wata tattaunawa da shirin da ake kira “Osasu Show” kwankwaso ya ce wannan ne karonsa na farko da ya ga yara masu kananan shekaru sun bin layin kada kuri’a.

A cewarsa inda hakan zai faru a zaɓen shekarar 2019 to da ƴan sauran jam’iyu za su ce da masu kada kuri’a dake da ƙarancin shekaru kan su fice daga wurin zaɓen.

“A dukkanin wani zaɓe ya kamata ace akwai fiye da jam’iya ɗaya dake takara idan kana da jam’iya fiye sama da ɗaya to jam’iyar A ba za ta bari B ta yi mata ko wanne irin mago-mago musamman kan batun mutanen da basu kai shekara 18 ba,”Kwankwaso ya ce.

You may also like