Akwai Wani Mahaukaci A Jihar Kano – Kwankwaso


Tsohon Gwamnan jihar Kano Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, kuma Sanatan Kano ta tsakiya ya nemi da aka taimaka masa da maganin warkar da mahaukata, domin warkar da wani Mahaukacin a jihar Kano. Kwankwaso ya yi wannan furuci ne yayin da wata kungiyar Masari Zalla daga jihar Katsina suka kai masa ziyara.

A cikin bayanan ayyukan kungiyar sun bayyana cewa, suna warkar da mahaukata domin taimaka musu su samu nagartacciyar rayuwa. Wanda da wannan furuci nasu Kwankwaso ya kada baki ya ce,

“Zan so ace kun taimaka mana da wannan lakanin warkar da mahaukata, domin mu ma a jihar Kano muna da wani Mahaukaci mai tsalle-tsalle, wanda idan aka warkar da shi jihar Kano za ta zauna lafiya”.

You may also like