Akwai yiyuwar fuskantar karancin man fetur yayin da dillalan mai ke shirin saka kafar wando ɗaya da NNPC


Kungiyar dillalan mai ta Najeriya ta yi barazanar janye aiyukanta a jihar Lagos daga ranar 11 ga watan Disamba kan zargin saba alkawarin yarjejeniyar da suka yi da kamfanin mai na kasa NNPC ya yi.

Kungiyar dillalan man fetur masu zaman lakansu ta Najeriya IPMAN, a jihar ta Lagos ta  zargi NNPC da laifin saba alkawarin sayar masu da mai kan naira 135 kan kowacce lita.

A wata sanarwa ranar Laraba, Alanamu Balogun shugaban kungiyar IPMAN a jihar yace kungiyar ta shirya saka kafar wando ɗaya da NNPC kan rashin samar da mai akai-akai a wajen ajiye mai dake Ejigbo.
Yace mambobin kungiyar sun kwashe watanni takwas suna tafka asara a gidajen mansu saboda saba alkawarin da kamfanin na NNPC yayi.

” Yanzu ana siyarwa IPMAN litar mai akan naira 141 daga  hannun yayan kungiyar manyan dillalan man fetur, DAPMAN, bayan kuɗin da zasu kashe na gudanarwa da kuma cajin banki.

” Hakan yasa da wuya mambobin kungiyar su iya sayar da litar mai a farashin da gwamnati ta kayyade na 145 kan kowacce lita.

“Yayin da NNPC yaƙi sayarwa da yayan kungiyar mai akai-akai sai gashi yana karkatar da man ga ya’yan kungiyar DAPMAN  inda yake sayar musu da man kan ₦117.

“DAPMAN kuma su sayarwa da IPMAN akan kuɗi ₦141.”

A karshe kungiyar tayi kira ga shugaban kasa Buhari da kuma majalisar ƙasa kan su saka baki a lamarin.

You may also like