
Asalin hoton, Getty Images
Kulob ɗin Saudiyya Al Nassr na sa rai ɗan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 37 zai kammala sa hannu don koma wa ƙungiyar nan da ƙarshen shekara. Tsohon ɗan wasan Manchester United ɗin zai sa hannu ne kan wata yarjejeniya ta tsawon shekara biyu a yuro miliyan 200.
Ɗan wasan gaban Brazil mai buga wa ƙungiyar Arsenal Gabriel Martinelli, mai shekara 21, na shirin sa hannu kan wani sabon kwanturagi da kulob ɗin nasa a kan fam 200,000-duk-mako.
Zakarun Faransa Paris St-Germain na sa rai, nan da ‘yan kwanaki za su sake tabbatar da zaman ɗan wasan gaban Argentina mai shekara 35 Lionel Messi a kulob ɗin. Kwanturagin gwarzon da ya lashe Gasar Kofin Duniya za ta ci gaba har lokacin zafi amma yana da damar ci gaba da tattaunawa da wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a wajen Faransa daga ranar 1 ga watan Janairu.
Ƙungiyar Arsenal da Atletico Madrid kowaccensu na da burin ɗaukar ɗan wasan tsakiyar da suka ci wa Argentina Gasar Kofin Duniya mai taka leda a Brighton Alexis Mac Allister, ɗan shekara 23.
Manchester United za ta biya fam miliyan 65 a matsayin sharaɗin sakin golan Porto ɗan ƙasar Portugal mai shekara 23 Diogo Costa idan suna son su ɗauke shi a ƙarshen wannan kaka.
Mai yiwuwa ne ɗan bayan Croatia Josko Gvardiol, mai shekara 20, ya ci gaba da zama a kulob ɗin ƙasar Jamus RB Leipzig a wannan kaka, kuma tanadin biyan yuro miliyan 110 ga mai son a saki ɗan wasan zai fara aiki cikin kwanturaginsa a shekara ta 2024.
Arsenal na ta nuna sha’awarta don ɗaukar ɗan wasan gefe na ƙasar Ukraine Mykhaylo Mudryk, mai shekara 21, idan an buɗe cinikayyar ‘yan wasa a watan Janairu, cewar daraktan wasanni na ƙungiyar ƙwallonsa ta yanzu Shakhtar Donetsk.
Golan Mexico Guillermo Ochoa, ɗan shekara 37, na sa ran tafiya ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Serie A a ƙasar Italiya Salernitana matsayin aro bayan kwanturaginsa ta ƙare a Club America.
Inter Milan ya hau teburin tattaunawa da ɗan bayan Italiya Alessandro Bastoni kan wani sabon kwanturagi, daidai lokacin da Manchester City da Tottenham ke nuna sha’awar aiki da matashin ɗan shekara 23.
Ɗan wasan tsakiya na Argentina Rodrigo De Paul, mai shakera 28, na daf da shiga Leeds daga kulob ɗin Udinese kafin ya tafi Atletico Madrid.
Akwai yiwuwar ɗan wasan gaban Blackburn na ƙasar Chile Ben Brereton Diaz, mai shekara 23, zai zauna a Ewood Park wannan watan Janairun don ba da dama ga zaɓin da yake da shi na tafiya aro a lokaci zafi mai zuwa.