Al Nassr na son haɗa Ronaldo da Ramos, mai son Enzo sai ya biya £106m



ramos

Asalin hoton, Getty Images

Al Nassr na ci gaba da ƙoƙarin ganin sun sake haɗa ɗan wasan gaban Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, da ɗan wasan bayan Paris St Germain mutumin ƙasar Sifaniya Sergio Ramos, mai shekara 36, a kulob ɗinsu. 

Manchester City na shirin biyan fam miliyan 10.6 a shekara don ɗan gaban AC Milan Rafael Leao, yayin da ƙungiyarsa ta Serie A, ita ma za ta riƙa biyan fam miliyan 6.2 duk shekara ga matashin ɗan shekara 23, wanda mahaifinsa ke tattaunawa da City

Tsohon babban jami’in kulob ɗin Birmingham City Xuandong Ren ya ce Man United da Chelsea duk sun yi yunƙuri ba tare da nasara ba wajen ɗauko ɗan wasan tsakiyar Borussia Dortmund na ƙasar Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, a 2020, duk da tayin biyan sa albashi mai kauri da suka yi. 

Babban jami’in kulob ɗin Shakhtar Donetsk Sergei Palkin ya ce “suna ci gaba da tattaunawa” da Arsenal kan ɗan wasan gefen Ukraine mai shekara 21 Mykhaylo Mudryk, bayan an ce wa Gunners albarka a tayin fam miliyan 55 da suka yi. 



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like