Al Nusra ta Syria ta yanke alaka da Al Qaeda


 

 

Shugaban kungiyar Al Nusra Abu Muhammad al Jolani ya nuna kansa a karon farko cikin wani hoton bidiyo tare da sanar da yanke alakarsu da babbar kungiyar Al Qaeda da suke aiki tare.

An dade dai Al Nusra na alaka da Al Qaeda a Syria, amma shugaban kungiyar Abu Muhammad Al Jolani ya yanke alakar tare da canza wa kungiyar suna zuwa Jabhat fatah al Sham, wato nasara akan Syria.

Shugaban ya aiko da sakon ta kafar bidiyo wanda kafar telebijin ta Al Jazeera ta nuna, kuma Wannan ne karon farko da shugaban na mayakan Al Nusra ya nuna kansa.

A cikin sakon ya bayyana godiyarsa ga kwamandojin Al Qaeda saboda fahimtarsu akan yanke alakar.

An dade dai ana hasashen rabuwar kungiyoyin biyu, kuma kungiyar Al Qaeda ta tabbatar da rabuwarsu da Al Nusra a wani sakon sauti na kakakinta Qaeda Ahmed Hassan Abu Khair.

Kuma ya ce sun ba Al Nusra ne damar kare muradunta na tabbatar da jihadi a Syria.
Wannan dai na zuwa ne bayan Amurka da Rasha sun amince su hada kai domin yakar mayakan Jihadi irinsu IS da al Nusra a Syria.

Al Nusra ta bayyana ne dai a 2012 bayan barkewar rikicin Syria a fakon 2011.

You may also like