al-Shabab sun kashe mutane shida a Kenya


 

 

Rahotanni daga kasar kenya na cewa mutane shida ne suka mutu a wani hari da makamai da ake zargin mayakan al-Shabab na kasar Somaliya ne suka kai a yankin arewa maso gabashin kasar.

Somalia al-Shabaab Kämpfer (picture alliance/AP Photo/M. Sheikh Nor)

Gwamnan jihar Mandera county Ali Roba, ya tabbatar da mutuwar mutane shida da sanyin safiyar ranar Alhamis wanda ake zargin ‘yan tawayen Somoliya ne suka kaddamar. Dama dai wannan yanki na Mandera na fuskantar hare hare daga masu kaifin kishin addini na kungiyar al-Shabab wadan da suka sha alwashin ci gaba da kai farmaki babu kakkautawa har sai gwamnatin kasar kenya ta janye dakarun sojin hadin guiwarta a kasar Somaliya.

To sai dai bayaga mutane shida da aka samu rahotannin tabbacin mutuwarsu kawo yanzu, babu wasu cikakkun bayanai da ke bada alamar dalilan kai harin da ga bangaren mayakan kazalika babu martanin jami’an tsaro kawo yanzu. Kasar kenya dai ta sha fama hare-hare sau da dama daga kungiyar al-Shabab.

You may also like