
Asalin hoton, Getty Images
A ranar Litinin 13 ga watan Janairu ne ƙasar Equatorial Guinea ta tabbatar da ɓullar cutar Marburg karon farko a ƙasar.
Cutar ta fara ɓulla ne a lardin Kie Ntem da ke yammacin ƙasar.
Kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutum tara, tare da samun mutum 16 da ke ɗauke da cutar a Equotorial Guinea, da kuma samun rahotonnin alamomin da ke nuna cewa mutum na ɗauke da cutar.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta aike da samfurin jini zuwa cibiyarta da ke ƙasar Senegal domin gwajin tabbatarwa.
Inda ɗaya daga cikin samfurin takwas ya nuna cewa cutar Marburg ɗin ce.
Ƙasar Ghana da Guinea sun tabbatar da ɓullar cutar a ƙasashensu cikin shekarun 2022 da 2021.
Haka kuma an samu rahotonnin ɓullar cutar a ƙasashen Angola da DR Kongo da Kenya da Afirka ta Kudu da kuma ƙasar Uganda.
Asalin hoton, Getty Images
Alamomin cutar Marburg
Alamomin cutar Marburg sun haɗar da
- zazzaɓi mai zafi da
- ciwon kai mai tsanani, da
- amai da kuma
- zubar da jini.
Yadda cutar ke yaɗuwa
Cutar Marburg ta yaɗu ne zuwa ga ɗan adam ta hanyar jemage, haka kuma cutar na cikin dangin ƙwayoyin cutar da ke haifar da cutar Ebola.
Cutar na yaɗuwa ne tsakanin mutane ta hanyar cuɗanyar ruwan da ke fita daga jikin masu ɗauke da cutar, kamar gumi(zufa) ko yawo (miyau) ko kuma bawwali da sauransu
Asalin hoton, @WHOAFRO
Shin cutar na da magani?
Cutar Marburg cuta ne da ke kisa, yawan waɗanda suka mutu a ɓullar cutar a baya sun kai kashi 24 zuwa 88 cikin 100.
Kawo yanzu cutar ba ta da riga-kafi, sannan kuma ba a kai ga gano maganinta ba.
To sai dai WHO ta ce yi wa mutum ƙarin ruwa da magance ɗaya daga cikin alamomin cutar kan taimaka wajen ganin mai ɗauke da cutar ya rayu.
Hukumar lafiya ta duniya ta tura tawagar ƙwararrun likitoci zuwa gabashin Equatorial Guinea domin taimakawa wajen daƙile yaɗuwar cutar
Haka kuma WHO ɗin na shirin aikawa da kayan aikin gwajin ƙwayoyin cutar zuwa ƙasar, ciki har da rigunan kariya 500 da likitocin za su yi amfani da su.