
Asalin hoton, OTHER
Matakin Shugaban Senegal na biyan tawagar kwallon kafar kasar alawus masu kauri ya haifar da cece-kuce.
Shugaba Macky Sall ya ce za su biya tawagar kudaden da suka yi alkawarin basu idan suka kai zagayen quarter-finals, duk da basu iya tsallake zagayen 16 ba.
Dama gwamnati ta yi wa Teranga Lions alkawarin kudade masu yawa idan suka kai zagayen quarter-finals, to amma sai gashi Ingila ta doke su 3-0 a zagayen kungiyoyi 16.
” Za mu biya duka kudaden da muka yi alkawarin bai wa tawagar,” in ji Shugaba Sall.
Rahotanni sun ce kudin da tawagar za ta karba ya kai dala miliyan 23.
Sai dai tsofaffin yan kwallon Senegal da wasu sanannu a fagen wasannin a kasar sun jefa ayar tambaya kan matakin.
Masu suka na cewa gwamnatin Senegal bata kamanta adalci ba, la’akari da yadda bata karrama sauran yan wasa da suka nuna bajinta ba a sauran wasanni.
An buga misali da Hamadel Ndiaye, dan wasan tsalle-tsallen Senegal da ya samu damar zuwa gasar Olympics, amma rashin kudin jirgi ya hana shi zuwa.
”Na kadu da naji makudan kudaden da aka ware don kai magoya baya Qatar,” in ji tsohon dan wasan.
Ya kara da cewa ”A 2019 da 2021, na so in shiga gasar tsere, amma tikitin jirgi ya yi min tsada.”
Sai dai tawagar ta Teranga Lions ce ke rike da kofin nahiyar Afrika, kuma ta yi nasarar tsallake zagayen rukuni a gasar Qatar 2022.
Kazalika Senegal ce kan teburin kasashe mafi kwarewa a iya kwallo a Afrika.