ALHAMDULILLAH: Wasu ‘Yan Bindiga A Jihar Zamfara Sun Karbi Da’awar Sheik Ahmad Gumi Sun Ajiye Makamansu


Gawurtaccen ‘dan bindiga mai garkuwa da mutane a jihar Zamfara Auwalun Daudawa tare da yaransa sun karbi da’awar Dr Ahmad Gumi sun ajiye makamansu na ta’addanci.

Auwalun Daudawa ya rungumi zaman lafiya, ya mika makamansa na yaki, ya mikawa rundinar ‘yan sanda bindigogi kirar AK47 guda 20 da sauran manyan bindigogi da harsashi da wasu miyagun makamai.

Bayan haka, yayi rantsuwa da Qur’ani shi da yaransa cewa har abada ba zasu sake komawa ga mugun halinsu na baya ba.

Auwalun Daudawa yana daya daga cikin manyan kungiyoyin ‘yan bindiga da suka sace daliban makarantar Kankara.

Muna rokon Allah Ya karbi tubansu, Ya shiryar da sauran barayin, Ya sakawa Dr Ahmad Gumi da gidan Aljanna. Amin.

You may also like