Shugaban tawagar likitocin gwamnatin tarayya da ke kula da mahajjata daga Nijeriya Dr Ibrahim Kana, ya sanar da rasuwar kimanin su 10 kafin a yi hawan Arfa na hajjin bana.
Haka kuma ya ce akwai wadanda aka kwantar a asibiti, amma an sallami yawancinsu.
Ya yi wannan bayani ne yayin da ya ke jawabi a lokacin taron da hukumar alhazan Nijeriya ta shirya wa wakilan kafar yada labarai na sashen Hausa, Muryar Amurka.
A jawabin, shugaban ya bayyana cewa kwana uku da zuwa arfa ne Allah ya yi wa Alhazan cikawa.Ya kuma bayyana cewa bincikensu ya gano cewa yawancinsu sun rasu sakamakon rashin lafiya ne kamar su hawan jini da ciwon sukari.
Likitan ya kuma bayyana cewa adadin rashin na bana bai kai na shekarun baya ba, ya ce ko a shekarar da ta gabata, mutane ashirin ne suka rasu a dai dai wannan lokaci.
cc: al’ummata