ALIYU ABUBAKAR: Dan Gaye Mai Tallan “Pure Water” 



A wasu lokutan yakan yi shigar gayu ko kuma ya yi shiga irin ta manyan ma’aikatan gwamnati dauke da robar saida ruwansa, inda yake yawo a yankun garin Mararrabar Abuja da jihar Nassarawa da kewayenta. Yakan shiga yankuna daban-daban da suka hada da ‘One Man Village’, Ado, Masaka, Nyaya domin tallar ruwansa.

Matashin mai suna Aliyu Abubakar, wanda dan asalin jihar Sokoto ne, wanda yake aji 4 a makarantar sakandire, ya bayyana cewa ya kudiri aniyar sayar da ruwan ne domin tallafawa karatunsa da samawa kansa kudin abinci, sutura da sauran dawainiyar yau da gobe.

Yanayin shigar da matashin yake yi a yayin da ya fito tallar ruwan ta sa yana samun ciniki fiye da yadda ake tsammani.

You may also like