Alkalai : Muna yaki ne da rashawa inji Buhari


 

Fadar shugaban Najeriya ta ce samamen ‘Yan sandan farin kaya ta kai tare da kama wasu manyan alkalan kasar, an yi hakan ne domin fadada rashawa amma ba akan bangaren shari’a ba na kasar ba.

Sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu ya fitar ta bayyana cewa an kai samamen a karkashin tsari na doka, kuma fadar shugaban ta samu tabbaci daga hukumar ‘yan sandan farin kaya da ke cewa akwai sammacin da ya bayar da damar yin hakan.

Kungiyar lauyoyin Najeriya ta bakin shugabanta Abubakar Mahmoud ta yi kakkausar suka da wannan matakin, yayin da ita kuma jam’iyyar adawa ta PDP ta ce kama alkalan abu ne da ya sabawa doka, tana mai cewa an yi garkuwa ne da su.

Amma a sanarwar da Garba Shehu ya fitar ya ce Shugaba Buhari Mutum ne da ke mutunta tsarin dimokuradiya da kundin tsarin mulki.

Hukumar DSS dai ta ce Jami’anta sun kwato makudan kudade a gidajen Alkalan da suka yi wa dirar mikiya a daren Juma’a zuwa wayewar safiyar Asabar a jihohin kasar 6 da kuma Abuja.

You may also like