Alkariyar fina-finai kitsin Abdulmumini ne


160722093350_yakubu_dogara_512x288_bbc_nocredit

A Najeriya majalisar wakilan kasar ta ce, aikin gina alkaryar fina-finai da gwamnati ta soke ba shugaban kasa ne ya kirkiro shi ba.

Majalisar ta ce, tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar Hon. Abdulmumini Jibrin ne ya cusa aikin cikin kasafin kudi ba tare da sani ko izinin bangaren shugaban kasa ba.

Tun bayan cire shi daga shugabancin kwamitin kasafin kudi ne dai Hon. Abdulmumini Jibrin yake yin tonon silili, yana zargin shugabannin majalisar da aikata cuwa-cuwa.

Hon. Abdulrazak Namdas shi ne kakakin majalisar wakilan, kuma ya shaida wa BBC cewa sauye-sauyen da ‘yan majalisar dokokin suka yi wa kudurin kasafin kudin da bangaren zartarwa ya gabatar musu ba laifi ba ne, hasali ma huruminsu ne, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.

You may also like