Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Allah ne kadai zai hade kan Nijeriya.
Kamar yadda shugaban ya ce, ba abu ne mai sauki ba mutane su hade kansu a kasa wadda take da yaruka sama da 450.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a jiya Talata a yayin da yake kaddamar da Jami’r Edo dake Iyambo a karamar hukumar Etsako a jihar Edo.