Allah Ya Yiwa Mahaifin Burutai Rasuwa



Labarin da muka samu yanzu yanzu na cewar Allah Ya yiwa Alhaji Yusuf Burutai rasuwa a Yau Jumma’a, wato Mahaifi ga shugaban hafsan sojojin najeriya, wato Laftanal Janaral Tukur Yusuf burutai.

Muna addu’a Allah Ya jikan sa da Rahama, kuma Ya gafarta masa, kuma Ya sa Aljanna makomar sa tare da dukkan Musulmai da suka riga mu gidan gaskiya. Amin summa Amin.

You may also like