Allah Ya Yiwa Tsohon Gwamnan Neja,  Abdulkadir Kure Rasuwa 



Inna Lillahi Wa Innah Ilahim Raji’un! 
Allah Ya yi wa tsohon gwamnan jahar Niger Engr Abdulkadir Kure rasuwa da yammacin yau a kasar Jamus.
Ana sa ran a gobe Litinin za a yi jana’izarsa a garin Minna bayan sallar Azahar. 
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa wanda na hannun daman marigayi tsohon gwamnan ne ya nuna kaduwarsa dangane da wannan rashin tare da baiyana tsohon amininsa da kasancewa mai son addini da aiwatar da gaskiya da zumunci a cikin al’umma. 
 Allah Ya jikansa da rahama.

You may also like