Tsohon Sanata daga jihar Zqmfara, Mukhtari Abdulkarim Mafara ya rasu. Ya rasu ne a daren ranar Juma’ar da ta gabata, a sakamakon mummunan hadarin mota da ya auku da shi a hanyar Kano zuwa Tsafe.
Wani mai fashin bakin al’amuran yau da kullum, ya bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi ga jihohin yankin Arewa maso yamma musamman jihohin Kebbi, Sokoto da kuma jiharsa ta Zamfara kasancewar mutum ne mai dattako da kuma son ci gaban al’umma.
Tuni dai aka yi jana’izarsa a garin Talata Mafara dake jihar Zamfara.