Allura Ta Tono Garma


Wani zazzafan cece-kuce ya barke a Amurka,tun bayan da jaridar Wall Street ta fallasa wani sirrin da shugannin kasar suka jima suna boye da shi dangane yadda aka yi,a ‘yan watannin da suka shude , Iran ta saki ‘yan kasarsu 5 da ta kama.

A ranar Larabar da ta gabata ce,jaridar ta ce shugabannin Amurka sun tura wa Iran zunzuruntun kudi dalar amurka milyan 400 domin sun fanshi rayunkan Amurkawan.

A lokacin da labarin ya fito fili, shugannin fadar White sun tabbattar da sahihancin lamarin tare da kawo gyara ,inda suka ce sun tura wa Iran din wannan kudin domin biyan wani tsohon bashi da ke tsakanin su.

A watan Janairun shekarar bara ce,manya-manyan kasashen duniya 6 wadanda suka hada da Amurka,Rasha,China,Ingila,da kuma Jamus suka hadu a babban birnin kasar Austria Vienna domin kawo karshen musayar yawu da suka dade suna yi game da batun nukiliyyar kasar Iran.Abinda yasa suka dage tankunkumin da suka sanya ma ta a tsawon shekaru da dama.

A washegarin wannan taron,sai aka samu labarin cewa kasar Iran ta saki wasu ‘yan kasar Amurka 5 da ta jima ta na kulle su.

A lokacin, kafafan yada labaran sun yada cewa Iran din ta dauki wannan matakin ne sakamakon rahamar da Amurka ta yi wasu firsunonin kasarta su 7.

A yanzu haka shugabannin Amurka na ci gaba da fadi tashin ganin sun wanke kansu daga duk wata tuhuma,amma tuni Amurkawa da ma sauran al’umar duniya suka dasa ayar tambaya kan yadda aka yi lamarin biyan bashi da na sakin fursunonin suka afku a zamani daya.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like