Almajiranci Na Barace-Barace Ya Saba Wa Tsarin Islama – Sarkin Musulmi Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III ya jaddada cewa dabi’ar almajiranci na barace barace a kan titina a tsakanin kananan yara da manya ya saba tsarin Musulunci inda ya kalubalanci gwamnonin jihohi su dauki matakin gaggawa na kawo karshen wannan tsarin.
Sarkin Musulmin ya nuna cewa Musulunci ya fifita sana’o’i da kuma samar da guraben karo ilimi kamar yadda Musuluncin ya kyamaci zaman banza da kasala wanda almajiranci na barace barace ya kunshi wadannan dabi’un.

You may also like