Almakura Ya Kaddamar Da Fara Sayar Da Takin Zamani Kan Naira 4000Gwamna Umaru Tanko Almakura na Jihar Nassarawa ya kaddamar da fara siyar da takin zamani mai rahusa akan kudi Naira 4000 a garin Jenkwe na Karamar Hukumar Obi dake jihar.

  AlmaKura yace duk da gwamnatinsa a yan shekarun da suka gabata tana siyan takin zamani ta kuma sayarwa da manoma kan kudi naira 5500  a bana sun yanke shawarar sayar da takin kan Naira 4000.

 ” Gwamnati ta zuba zunzurutun kudi har naira biliyan daya wajen siyan takin kan kudi Naira 5500 akan kowanne buhu,amma duba da halin da manoma suke ciki.mun yanke shawarar zaftare farashin zuwa 4000, a zahirance yaci ya zarce haka duba da yadda farashin kayayyaki suka tashi,da kuma tsadar canjin kudaden kasashen waje, amma gwamnatin na sane da halin wahala da mutane suke ciki,”yace  

You may also like