Almubazaranci da Almundahana da Rashin Hangen Nesa Suka Ruguza Tattalin Arzikin Najeriya – Mailafiya


Farfasa Mailafiya malamin ilimin tsimi da tanadi a nan Amurka yana ganin almubazaranci da almundahana da rashin hangen nesa a bangaren shugabannin kasar suka haddasa mummunan sakamakon rugujewar tattalin arzikin kasar

Farfasa Mailafiya ya bada dalilan da suka sa tattalin arzikin Najeriya ya zama abun da ya zama yayinda yake zantawa da Muryar Amurka.

Yace abu na farko da ya kawo koma bayan tattalin arzikin Najeriya , inji Farfasa Mailafiya shi ne rashin hangen nesa. Idan an samu kudi ba za’a kashe kan gina masana’antu ba ta yadda duk abun da kasar ke bukata zata sarafasu a gida ba sai ta shigo dasu daga waje ba, amma sai a kashe akan abubuwan banza.

Akwai kuma matsalar sace kudi. Tun daga matakin kananan hukumomi zuwa shugabancin kasar duk wanda ya hau kan mulki abun da ya sa gaba shi ne wawure dukiyar kasar, ya gina kansa da iyalansa da sauran ‘yanuwansa. Abun takaici ma shi ne bayan an sace kudaden ba za’a yi anfani dasu ciki ba sai a fita dasu waje.

Wani abun kuma shi ne rashin kafa wani tsari na musamman na cigaban tattalin arzikin kasa. Lokacin da aka karbi mulki daga turawan mulkin mallaka akwai tsarin da ake yi na gina kasa. Ana yin tsarin na shekara biyar biyar. Daga karshen kowace shekara biyar sai a duba a ga inda aka cigaba da inda aka kasa.Duk wadannan an bari. Kowace gwamnati ta hau mulki sai ta fara daga farko maimakon ta cigaba daga inda gwamnatin baya ta tsaya.

Dangane da matakan gaggawa da ya kamata gwamnatin Buhari ta fara dauka, Farfasa Mailafiya yace abun da ya kamata a fara yi shi ne inganta da gina wutar lantarki domin idan babu wuta, to babu wata masana’anta da zata yi aiki. Ba za’a samu habakar masana’antu ba ko gina sabbi. Abu na biyu shi ne maganar cin hanci da rashawa wanda shugaba Buhari ya sa gabansa gadan gadan. Dole ne a yaki wawurar kudi da ake yi. Idan za’a yi da gaske kudaden da aka samu a gina wutar lantarki dasu. A sa wasu wurin gina masana’antu. Yin hakan zai sa mutane su samu ayyukan yi lamarin da zai habaka tattalin arzikin kasa.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like