Al’ummar Jihar Neja Ta Arewa Zasuyi Wa Sanatan Su Kiranye A Karo Na BiyuSanata mai wakiltar Jihar Naija ta Arewa Dakta Aliyu Sabi Abdullahi (Baraden Borgu) kuma mai magana da yawun majalisar dattijan Nijeriya, na fuskantar barazanar kiranye a karo na daga al’ummar mazabarsa. 

Al’ummar yankin na ganin irin mulkin kama karya da yake yi musu bai dace a ce shi ne yake wakiltar kan al’amuran da suka shafi cigaban rayuwar su ba. Don haka ne ma a yanzu haka suka fitar da gwanin su a zaben shekara ta 2019 mai zuwa daga yankin karamar hukumar Rijau, wato Alhaji Shehu Saleh mai lakabi da Slow. 

Sun yi zargin cewa, tun da Sanatan ya je yakin neman zabe bai sake komawa wasu kananan hukumomi dake yankin mazabar Naija ta Arewa ba, musamman ma dai karamar hukumar Rijau. 

Wata majiya ta shaidawa Zuma Times Hausa cewa ko a bayan wata uku da suka gabata, wani taro ya taba kulluwa a garin Kontagora da hadin kan kananan hukumomi 8 na yankin, domin kulla yadda za a yi masa kiranye, amma abin bai kai ga nasara ba. 

Al’ummar mazabar dai na kukan Sanata Barade ba ya zama a jihar ma ta Naija, kullum yana Abuja ko kuma jihar Kwara, can wajen mai gidansa Bukola Saraki, shugaban majalisar dattijai. 

You may also like