Al’ummar kasar Somaliya na bukatar agajin gagawa. | Labarai | DWAntonio Guterres wanda ya kai ziyarar gani da ido a kasar da ke gabashin Afirka ya ce, Somaliya na cikin wani hali da ke bukatar agajin gagawa a daidai lokacin da suke kuma fama da ayyukan ‘yan ta’adda.

A wata ganawa da manema labarai da ya yi tare da shugaban kasar Hassan Sheikh Mahmoud, Guterres ya ce, ya je kasar ce domin ya gani da idonsa ya kuma sanar wa duniya halin da al’ummar Somaliya ke ciki.

Al’umma a Somaliya dai na a cikin wani hali, inda aka tabbatar da akwai sama da mutane miliyan 6 da ke fama da matsananciyar yunwa, halin da ba a taba ganin irin shi ba a tarihin farin da kasar ta shiga a baya.
 

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like