Shugaba Muhammad Buhari ya bayyana cewa a yau mutane ba su dauki cin amana a matsayin laifi ba a maimaikon haka rashin amana ya zama wata dabi’a a tsakanin al’ummar.
Buhari ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da bude sabon hedkwatar hukumar EFCC inda ya ce yaki da rashawa na da matukar wahala saboda ya shafi rassa daban daban na rayuwar al’umma.
A nasa bangaren, Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya yi ikirarin cewa har yanzu akwai milyoyin ‘yan Nijeriya wadanda ke da gaskiya da rikon amana ba ya ga Shugaba Muhammad Buhari.