Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Anna Foster
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC daga Derna
Wani likita sanye da takunkumi ya sunkuyar da kai cikin baƙar ledar sanya gawa, kuma a hankali yana jujjuya ƙafafuwan mutumin da ke ciki. “Da farko sai mun tantance shekaru, da jinsi da kuma tsawonsa,” yana bayani.
“Yanzu ya shiga matakin ruɓewa, saboda ruwan da ya sha.”
A wani filin ajiye motoci na wani asibiti da ke Derna, birnin gabashin, ana duban tsanaki ga bayanan ƙarshe na ɗaya daga cikin mutanen da bala’in ya ritsa da su, don shigarwa a littafi.
Wannan a yanzu yana ɗaya daga cikin ayyuka mafi muhimmanci a nan, kuma ɗaya daga cikin mafi tayar da hankali. Ba a iya gane ko wane ne mutumin ba, bayan ya shafe tsawon mako ɗaya a cikin teku. Da safiya ne ruwa ya tunkuɗo gawarsa bakin teku.
Ƙwararru suna tantance gangar jiki sannu a hankali don gano wasu tabbunan da za a iya shaida mutumin da su, sannan an ɗauki samfurin jikin, don gwajin DNA. Hakan na da matuƙar muhimmanci, saboda ko za a samu wani dangin mutumin da har yanzu ke raye.
Gwamnatin da ƙasashen duniya ke marawa baya ta ce gine-gine sama da kashi ɗaya cikin huɗu na Derna, ko dai sun lalace ko kuma sun rushe a bala’in.
A hukumance, har yanzu akwai mutane sama da 10,000 waɗanda suka ɓata, cewar alƙaluma daga Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya kan harkokin Jin Ƙai.
Ƙungiyar ba da agaji ta Red Crescent ita ma ta fitar nata alƙaluma.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce yawan mutanen da suka mutu zuwa yanzu ya kai 11,300. Alƙaluman ƙarshe har yanzu ba za a iya fayyace su ba ƙarara – ko da yake wani abu da yake tabbas shi ne matuƙar girman wannan bala’i.
Mohammed Miftah yana ji a cikin zuciyarsa cewa danginsa na cikin waɗanda iftila’in ya ritsa da su.
Lokacin da ya don gano ƙanwarsa da mijinta a gidansu bayan ambaliyar ruwan, sai ya taras ruwa ya yi awon gaba da shi.
Tun daga lokacin dai, bai ji komai daga gare su ba. Ya nuna mini wani bidiyo da ya ɗauka lokacin da ruwa ya yi toroƙo, ruwan taɓo yana kwararowa ta ƙofar gaba na gidansa.
Igiyar ruwa ta ɗauko wata mota, wadda ta kutsa cikin wani ɗan sarari, sannan ta tokare wurin gaba ɗaya.
“Na ga motocin da ruwa ya taho da su, inda na fito daga cikin gida da gudu,” kamar yadda ya riƙa tunowa.
“Ina jin shi kenan, na riƙa jin cewa mutuwa ta zo. Muna iya ganin maƙwabtanmu suna karkaɗa mana tocilan. Zuwa ɗan wani lokaci ƙalilan, sai aka daina ganin tocilan, duk sun ɓata.
“Wannan abu ne mai tsanani.”
Asalin hoton, Reuters
Sabrine Ferhat Bellil ta rasa ɗan’uwanta, da matarsa da kuma ‘ya’yansu biyar lokacin da gawurtacciyar guguwar ta auka wa birnin.
Yayin da kayan agajin ƙasashen duniya ya fara isa ƙasar da gaske, ministan lafiya na gwamnatin gabashin Libya ya sanar da cewa ma’aikatan ceto na ƙasar Girka huɗu sun mutu sanadin wani hatsari a kan titin zuwa Derna.
Ƙarin sha huɗu sun ji raunuka. Suna kan hanyar zuwa wurin takwarorinsu ne waɗanda tuni suka isa can daga ƙsashen Faransa da Italiya.
Ƙasashen Kuwait da Saudiyya su ma sun tura ɗumbin kayan agaji.
Mohammed Miftah yana fargabar wasu a danginsa na cikin mutanen da suka rasu
Mataki na gaba shi ne a tabbatar da ganin cewa an yi amfani da kayan ta hanyar da ta dace kuma a samu daidaito.
Abdullah Bathily, shugaban jami’an ba da tallafi na Majalisar Ɗinkin Duniya a Libya, ya faɗa wa Sashen Larabci na BBC cewa ƙasar a yanzu tana buƙatar samar da wani fayyataccen tsari don gudanar da duk gudunmawar ƙasashen duniya da suke samu.
Damuwar suke da ita, ta taso ne sakamakon sanannen ƙalubalen da ake da shi na yin aiki tare tsakanin gwamnati a birnin Tripoli wadda ƙasashen duniya suke mara wa baya da kuma takwararta da ke gabashin Libya.
Asalin hoton, Reuters
Wata mota da ta lalace a can saman wani gini bayan mummunar ambaliyar ruwan Derna
Can a tsakiyar Derna, akwai cibiyoyin da aka dallare da haske a tsakiyar ɓaraguzai da taɓon da suka mamaye birnin.
A wani titi, ɗaruruwan tufafi masu launuka iri daban-daban ne aka tara tsib-tsibi.
A tsallaken titi, an kafa wani dogon layi yayin da ake bai wa mutanen da suka kuɓuta man fetur.
A lokacin da gudunmawar kaya ke ci gaba da shigowa, wani mutum ya iso, inda ya ɗora wani kwalin mayafai da ɗan kwali a kan ƙafar wata dattijuwa.
Ya sumbace ta a kai cike da nuna ƙauna, daidai lokacin da ta yi murmushi kuma ta fara ɗaɗɗagawa don zaɓar ɗaya.
Waɗannan ‘yan Libya ne masu taimakawa ‘yan Libya a ɗaya daga cikin bala’o’i mafi muni da suka taɓa rayuwarsu.
Hukumar kula da Ƙaura ta Duniya ta ba da adadin 38,000 zuwa 30,000 a matsayin mutanen da suka rasa muhallansu a gabashin Libya a Derna kaɗai.