Ambaliyar ruwa ta afka kan taron mabiya addinin Hindu | Labarai | DWAna ci gaba da laluben gano wasu mabiya addinin Hindu da suka bata bayan wata munmunar ambaliyar ruwa da ta afkawa taron mabiya addinin Hindu. Ruwan sama kamar da bakin kwarya ne ya haddasa ambaliyar, a yankin Kashmir,  akwai wasu da dama da suka ji rauni da tuni aka kwashe su da jirgin sama mai saukar ungulu zuwa asibiti.

Firaiministan Indiya Narendra Modi, kasar da ke jayayya da Pakistan kan yankin na Kashmir, ya baiyana takaicinsa kan aukuwar iftala’in tare da jajantawa iyalan wadanda lamarin ya shafa, yana mai cewa, za a taimaka musu da duk abin da suke bukata. 
 You may also like