Ambaliyar ruwa ta ci Birnin Kebbi


120724133126_jos_flooding_2_512

Rahotanni daga jihar Kebbi a arewacin Najeriya, na cewa daruruwan mutane na fama da rashin matsuguni da kuma abinci, bayan da ambaliyar ruwa ta mamaye unguwanni da dama a Birnin Kebbi babban birnin jihar.

Lamarin dai ya faru ne sakamakon ruwa kamar da bakin kwarya da aka tafka a garin da safiyar Talata.

A hukumance babu rahoton asarar rayuka, amma dabbobi da yawa sun halaka a lamarin.

Haka kuma akwai wasu mutane musamman yara da har yanzu ba a gani ba wadanda ake fargabar ambaliyar ta yi awo gaba da su.

Gwamnan jihar Abubakar Atiku Bagudu ya shaida wa BBC cewa toshewar magudanun ruwa ya taimaka wajen faruwar wannan matsalar, ko da yake an jima ba a ga ruwan sama kamar haka ba a garin.

Hukumomi sun ce suna bakin kokarinsu domin taimakawa wadanda lamarin ya shafa da kuma gano inda wadanda ba a gani ba suke.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like