Wata ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutum guda da kuma lalata gidaje kusan 1000 Sakamakon ruwan sama mai karfin gaske da aka yi a karamar hukumar Kura na jihar Kano.
Kamfanin dillanci Labaru na Nijeriya ya ruwaito cewa ƙauyakun da al’amarin ya shafa sun hada da Dannafake, Iyatawa, Kaniyaka, Zagazagi, Tofa and Yadagungume inda a halin yanzu mutanen da abin ya shafa suka nemi mafaka a gidajen ‘Yan uwansu.