Ambaliyar Ruwa Ta Shafi Kananan Hukumomi 99 a Nijeriya


flood-e1474631636497-1

 

Hukumar kula da harkoki ruwa a Nijeriya (NIHSA) ta fitar da wani rahoto a jiya Alhamis da ke nuna cewa ambaliyar ruwa ya shafi kananan hukumomi guda 99 a jahohi 30 a fadin kasar, kuma ya hallaka mutane 29 izuwa yanzu.

Daraktan hukumar NIHSA, Moses Beckley ya bayyana haka ne a  wani taron wayar da kai akan hasashe da kuma kare kai daga ambaliyar ruwa da hukumar ta shirya a wajen saukar baki na Halims da ke Lokoja.

A fadar Mr Beckley, sun shirya taron ne domin su wayar da kan jama’a duba da yadda faruwar ambaliyar ruwa ya yi yawa a kasar.

Karanta Wannan:Babu Hannaye Babu Kafafu, Amma Yana Jagorantar Al’umma

Jahohin da ambaliyar ruwan ta shafa sun hada da Kaduna, Niger, Nassarawa, Benue, Edo, Jigawa da sauransu.

Daraktan ya yi kira ga gwamnotoci a kowanne mataki na kasar da su sauya yanayin gina ginan magudanan ruwa su kuma sauyawa mutanen da ibtila’in ya shafa gurin zama.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like