Ambaliyar  RuwaTa Lalata Gidaje 100 A Garin Gwarzo Dake Jihar Kano 



A kalla gidaje 100 ne suka lalace bayan wani mamakon ruwa a karamar hukumar Gwarzo dake jihar Kano, bayan wani mamakon ruwan sama a ranar Talata. 

Ambaliyar ruwar ta raba mutane da yawa da muhallansu a unguwannin da abin ya shafa. 

Wani shedar gani da ido Mallam Ibrahim Shuaibu ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, cewa unguwannin da ambaliyar tafi kamari sun hada da Sabuwar unguwa,  Abuja Quaters da kuma unguwar Katambawa dake garin na Gwarzo. 

Har ila yau ruwan ya lalata katangar Sakatariyar karamar hukumar yayin da motoci da yawa suka nutse  a ruwa. 

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano  (SERERA), Alhaji Aliyu Bashir ya tabbatar da faruwar lamarin, amma yace bashi da adadin gidajen da suka lalace. 

Bashir  yace tuni aka tura jami’ai daga hukumar ta SERERA  da kuma hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA domin su tantance irin barnar da ruwan yayi. 

You may also like