Amirka: Cecekuce kan kalaman Donald Trump bisa mata


 

 

A Amirka wani sabon cece-kuce ne ya taso dangane da wasu kalamai na kaskantar da mata da dan takarar neman shugabancin kasar a karkashin inwar jam’iyyar Republican wato Donarld Trump ya furta.

USA Republikaner Wahlkampf Donald Trump in Reno, Nevada (Reuters/M. Segar)

Jaridar Washington Post ce ta wallafa wani tsohon faifayin bidiyo na shekara ta 2005, da inda a cikin aka nadi muryar Donald Trump,  ga alama ba tare da saninsa ba inda yake cewa idan dai mutun na da wani matsayi to kuwa yakan iya yin abin da ya ga dama da mata. Ga ma dai kadai daga cikin kalaman nasa:

“Donald Trump kenan ke cewa na yi kokarin in yi lalata da ita kuma matar aure ce.Ba irin jan hankalin da ban yi mata ba, amma dai ban yi nasara ba”

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da ake samun Donald Trump yana furta kalamai na wulakanta mata. Tuni ma dai wasu daga cikin kusoshin jam’iyyar Republican suka yi tir da Allah wadai da kalaman nasa.

Masu lura da harakokin siyasar kasar ta Amirka na gani wannan kalamai na Donald Trump za su kasance wani babban makami da abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton za ta iya amfani da shi kan Donald Trump din a mahawara ta gaba da za ta hada ‘yan takarar neman shugabancin kasar ta Amirka.

Sai dai tuni Donal Trump ya fito ya nemi gafara tare da mayar wa Hillary Clinton da martani ta hanyar tunatar da ita irin abin da ya kira kaurin sunan da mijinta wato Bill Clinton  ya yi wajen aikata ayyukan masha’a da mata a lokacin da yake shugabancin kasar ta Amirka.

You may also like