Amirka- Clinton mai tsattsauran ra’ayi ce –  Trump


 

images

 

 

 

Dan takarar shugabancin Amurka na jam’iyyar Republican Donald Trump ya ambaci abokiyar takararsa ta jam’iyyar Democrat, Hilary Clinton a matsayin mai tsatssaurar ra’ayi.

Trump dai yana magana ne a wajen yakin neman zabe a Mississippi, inda ya ke kokarin jan hankalin tsuraru a Amurka domin su zabe shi.Yace Clinton na amfani ne da launin fatar mutane domin su zabeta kawai, amma ba dan tana daukar su a matsayin mutane da ya kamata a kula da makomar su ba.

Trump ya kuma ce Clinton da jami’yyarta Democrat na yin amfani ne kawai da Amurkawa ‘yan asalin Afirka don cimma bukatar cin zabe.

To sai dai tuni Hilary Clinton ta maida masa martani, inda ta zarge shi da cewa yana maida hankali kan kalaman kyamatar tsuraru da kuma nuna wariya.

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a baya bayannan ta nuna cewa kaso biyu cikin dari ne kawai nabakaken Amurkawa suka ce za su zabi Donald Trump.Ana dai tafka zazzafar hamayya tsakanin ‘yan takarar na shugabancin Amurka a zaben da za a yi a karshen shekarar nan.

You may also like