Ma’aikatar Harkokin Waje ta Amurka ta amince da a sayarwa da Saudiyya manyan tankokin yaki da suke dauke da makamai da kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 1.15.
Sanarwar da aka fitar daga Hukumar hadin Kai ta Tsaro ta Amurka na cewa, akwai tankokin yaki guda 130 samfurin Abrahams da kuma rufaffun motocin harba bam guda 20. Akwai bindigu da sauran makamaimda darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan dubu 1 da miliyan 150 da aka sayarwa da Saudiyya.
Sanarwar ta ce, wannan mataki da aka dauka na karkashin hadin kan Amuka da kasashen duniya kuma zai kara taimakawa wajen tsaron kasar, kuma hakan zai kara dankon zumunci tsakanin Amurka da rundunar sojin Saudiyya.
Haka zalika sanarwar ta kara da cewa, an sanarwa da majalisar domkokin Amurka batun sayarwa da saudiyya makaman.
Majalisar dai na da kwanaki 30 na nuna kin amincewa da sayar da makaman.