Amnesty ta zargi kasashe masu arziki da kin taimakawa ‘yan gudun hijira


 

 

 

Kungiyar Kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta zargi kasashen da suka fi arziki a duniya da kin taimakawa baki ‘yan gudun hijira, yayin da ta ke cewa yanzu haka kasashe matalauta 10 ke daukar nauyin kashi 56 na bakin.

Rahotan kungiyar Amnesty International da ya yi nazari kan ‘yan gudun hijira miliyan 21 da yanzu haka ake da shi a duniya, ya ce kasashen da ke makwabtaka da inda ake samun rikice rikice ne ke daukar nauyin bakin, yayin da kasashe masu arziki suka kauda kan su.

Sakatare Janar na kungiyar Salil Shetty ya ce an barwa kasashe ‘yan kadan nauyin abinda yafi karfin su, na karbar kashi 26 na bakin.

Jami’in ya bayyana halin da ake ciki a matsayin abinda ba mai dorewa bane, ganin irin yadda miliyoyin mutane ke tserewa kasashen da ake yaki irin su Syria da Sudan ta kudu da Afghanistan da Iraqi.

Amnesty ta bayyana kasashen da suka fi daukar nauyin bakin da suka hada da Jordan mai dauke da miliyan biyu da 700,000, sai Turkiya mai miliyan biyu da rabi, Pakistan da Lebanon masu sama da miliyan daya da rabi.

Sauran kasahsen sun hada da Iran da Habasha da Kenya da Uganda da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da Chadi.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like