Amnesty ta zargi Sojin Najeriya da kashe ‘Yan Biafra 150


 

Kungiyar Kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta zargi jami’an tsaron Najeriya da kasha masu fafutukar neman kasar Biafra sama da 150 daga bara zuwa bana. Amma rundunar sojin Najeriya ta karyata rahoton.

Kungiyar ta yi zargin cewar, jami’an tsaron sun amfani da harsasai da kuma karfin da ya wuce kima wajen afkawa masu zanga-zangar.

Amnesty ta ce rahoton da ta fitar ya biyo binciken da ta gudanar da kuma hirarraki da mutane kusan 200 da hotuna da bidiyo kusan 200 da suka tabbatar da zargin.

Amma Rundunar Sojin Najeriya ta karyata rahoton kungiyar inda Kanal Usman Kukasheka ya ce babu gaskiya a rahoton da ya danganta a matsayin bacin suna ga sojin kasar.

Kanal Usman Kukasheka ya shaidawa RFI Hausa cewa babu wani lokaci da jami’ansu suka kashe adadin mutane kusan 150.

Kukasheka ya ce kungiyar Amnesty ta ki fadin barnar da masu zanga-zangar neman ‘yancin Biafra suka yi inda ya ce sun kashe ‘Yan sanda biyar a ranar 30 na Mayun bana tare da salwantar da dinbin dukiyoyin jama’a

You may also like