Amurika, Faransa da Birtaniya sun kaddamar da hare-hare ta sama kan kasar Siriya


Kasashen Amurika, Faransa da kuma Birtaniya sun kaddamar da hare-harem makami mai linzami kan kasar Siriya.

Wannan dai wani martani ne kan zargin da ake yi cewa gwamnatin shugaba Bashar Al-assad ta kai hari da makami mai guba kan fararen hula.

Da yake sanar da fara kai harin ranar Juma’a a fadar White House, shugaba Donald Trump na Amurika ya bayyana harin a matsayin wani mataki da aka fara dauka na dakatar da shugaba Bashar Al-assad.

Sai dai tun da fari kasar Rasha ta yi gargadin mayar da martani matukar kasashen suka kaddamar da hari akan kasar ta Siriya.

A wata sanarwa ranar Asabar rundunar sojan kasar ta ce makami mai linzami 110 aka harba sai dai na’urar kakkabo makami mai linzami ta kasar ta samu nasarar kakkabo da yawa daga cikinsu amma duk da haka wasu sun samu nasarar sauka inda aka harba su ciki har da wata cibiyar binciken kimiyya dake birnin Barzeh.

You may also like