Amurka Da Birtaniya Sun Kadu Da Nasarar Sojojin Syria A Kan ‘Yan Ta’adda A Aleppo


 

 

Sakatarorin tsaro na kasashen Amurka da Birtaniya sun nuna kaduwa matuka dangane da nasarar da sojojin Syria karkashin jagorancin Bashar Assad suka samua kan ‘yan ta’adda a birnin Aleppo.

Jim kadan bayan wani jawabi da shugaba Bashar Asad na Syria ya yi a jiya da ke taya al’ummar Syria muranar samun nasara a kan ‘yan ta’adda a Aleppo, sataren tsaro na Amurka Ash Carter tare da takwaransa na Birtaniya Michael Fallon, sun gudanar da wani taron manema labarai na gaggawa  a birnin Landan, inda suka bayyana takaicinsu matuka dangane da yadda sojojin Syria suka samu nasara a kan ‘yan ta’adda da ke rike da Aleppo fiye da shekaru 3.

Inda suka bayyana cewa duk da wannan nasara da Assad ya samu a Aleppo, ba zai ci gaba da shugabancin kasar Syria ba, za su ci gaba da matsa lamba a kansa har sai ya safka daga shugabancin kasar.

Kasashen Amurka da Biratniya gami da Faransa dai su ne manyan kasashen da suke bayar da kariya ga ‘yan ta’adda a Syria, yayin da kasashen Saudiyya, Qatar da UAE suke yi musu cinikin makamai na biliyoyin daloli da ake aike wa ga ‘yan ta’addan, a cikin Syria da kuma Iraki, tare da biyan kudaden horon da ake baiwa ‘yan ta’addan,a  cikin kasashen Turkiya da Jordan.

Ita ma a nata bangaren kungiyar da ake kira kungiyar hadin kan kasashen larabawa, a zaman da wakilanta suka gudanar jiya a birnin Alkahira na kasar Masar, sun yi Allawadai da nasarar da sojojin Syria suka samua  akan ‘yan ta’adda a birnin Aleppo, yayin da Kasar Kuwait  ta yi kiran kiran wani zaman gaggawa a ranar Litinin mai zuwa na ministocin harkokin wajen kasashen larabawa, domin tattauna mataki na gaba da za su dauka bayan murkushe ‘yan ta’adda da sojin Syria suka yi a Aleppo.

You may also like