Amurka: An kashe wani babban jagoran Alqa’eda a Siriya


 

 

Kakakin Ma’aikatar Tsaro ta Amurka Pentagon Peter Cook ya sanar da cewa, an kashe babban jagoran kungiyar ta’adda ta Alqa’eda Al-Masri a kasar Siriya a ranar 18 ga watan Nuwamba.

Al-Masri wanda dan asalin kasar Masar ne ya tafi kasar Siriya bayan aiki tare da Alqa’eda a Afganistan inda ya zama daya daga cikin manyan jagoririn kungiyar a kasar.

An bayana cewa, an kashe Al-Masri a kusa da garin Sirmata a wani hari ta sama da aka kai.

Al-Masri ya taka rawa sosai wajen kai hare-hare kan dakarun Amurka a Afganistan.

Cook ya sanar da cewa, kashe Al-Masri ya zama wata abbar nasara a yaki da suke da ta’addanci a yankin.

You may also like