Amurka na barazanar hukunta Uganda saboda dokar hukunta masu luwaɗiJoe Biden

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaban Amurka, Joe Biden

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta yi gargaɗin cewa za ta hukunta Uganda ta fannin tattalin arziƙi matuƙar aka tabbatar da dokar tsananta wa masu neman jinsi ɗaya.

Mai magana da yawun majalisar tsaron Amurka, John Kirby ya shaida wa manema labaru cewar “za mu duba mu ga wane mataki za mu ɗauka, kamar ta ɓangaren tattalin arziƙi, matuƙar aka amince da fara aiki da dokar.”

“Saboda haka za mu duba. Har yanzu ba mu ɗauki mataki ba, amma muna lura da duk abin da ke gudana. Muna fatan cewa ba za a amince da dokar ba, mu ma shi ke nan ba sai mun ɗauki mataki ba.”

Dokar dai ta tanadi hukuncin ɗaurin rai-da-rai a kan mutanen da suka bayyana kansu a matsayin ƴan luwaɗi a Uganda. Haka nan kuma zai iya kai wa ga hukuncin kisa.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like