
Asalin hoton, Getty Images
Kocin rikon kwarya na Amurka, Anthony Hudson ya ce yana tattaunawa da Folarin Balogun, domin ya koma buga wa kasar tamaula.
Mai shekara 21, wanda iyayensa daga Najeriya suka haife shi a Amurka, wanda aka raina a Ingila, zai iya zabar kasar da zai murza mata leda.
Balogun, wanda ke buga wasan aro a Reims daga Arsenal ya buga wa tawagar matasan Ingila tamaula.
Ba zai buga wa tawagar Ingila ta matasa ‘yan 21 ba, bayan da yake jinya.
Balogun ya ci kwallo 17 a Reims a Ligue 1 a kakar nan, saura biyu ya tarar da Kylian Mbappe da Jonathan David a yawan cin kwallaye a Ligue 1.
Dan wasan Arsenal, Balogun mai wasannin a Faransa na taka rawar gani a Ligue 1.
Tun can baya ya fada cewa a shirye yake ya tattauna da wakilan Najeriya idan Super Eagles na bukatarsa, zai kuma iya buga wa babbar tawagar Ingila wasa.
An gayyaci Balogun cikin tawagar Ingila ta ‘yan shekara 21, domin buga wasan sada zumunta da Faransa da Croatia a watan Maris, amma yanzu yana jinya.
Tawagar Amurka tana Florida a shirin da take na buga Concacaf Nations League a Grenada.