
Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta samu damar amfani da ƙarin sansanonin soji huɗu da ke Philippines wanda hakan zai ba ƙasar damar sa ido kan abubuwan da China ke yi kusa da Taiwan.
Sakamakon wannan yarjejeniya, Washington ta cike giɓin da take da shi na ƙawancen Amurka wanda ya taso tun daga Koriya ta Kudu da Japan daga arewa zuwa Australia daga kudu.
Dama can inda aka samu saɓani shi ne ta ɓangaren Philippines wadda ke da iyaka da wurare biyu masu muhimmanci mafi girma wato Taiwan da kudanci Tekun China.
Yarjejeniyar, wadda ta wani ɓangaren take dawo da halin mulkin mallaka wadda ta taba shiga a baya daga Amurka.
“Babu wani lamari da ke faruwa a Kudancin Tekun China wanda ba shi buƙatar Philippines,” in ji Gregory B Poling, daraktan tsangayar nazarin kudu maso gabashin Asia a cibiyar horas da dangantakar ƙasa da ƙasa da ke Washington.
“Amurka ba ta buƙatar sansanoni na din-din-din. Batun wurare ne ba sansanoni ba.”
Tuni dama Amurka ta samu zarafin iko da wurare biyar a ƙasar ƙarƙashin wata yarjejeiniya ta inganta haɗin kan tsaro.
Ƙara samun ikon kamar yadda wata sanarwa da Washington ta fitar, zai bayar da dama a samu ƙarin tallafi domin daƙile sauyin yanayi da kuma wasu nau’in bala’i, mai yiwuwa ana nufin daƙile China daga duk wani hari a yankin.
Sanarwar ta zo ne bayan da sakataren harkokin tsaro na Amurka Lloyd Austin ya haɗu da shugaban Philippine Ferdinand “Bongbong” Marcos Jr a Manila a ranar Alhamis.
Amurka ba ta yi ƙarin bayani kan wuraren da sabbin sansanonin suke ba amma akwai yiwuwar uku daga cikinsu suna a Luzon, wanda tsibiri ne da ke kusurwar arewacin Philippines, wanda nan ne gari ɗaya da ke kusa da Taiwan idan ba a ƙirga da China ba.
Asalin hoton, Getty Images
China ta caccaki wannan yarjejeniyar, inda ta ce “Ayyukan Amurka za su iya saka fargaba a yankin da kuma kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankim”.
A halin yanzu, Amurka na neman samun wuraren da za a iya yin ayyuka ba ma su yawa ba da suka haɗa da kai kayayyaki da sa ido idan ana buƙata, a maimakon jibge sojoji masu yawa a wuri.
Hakan na nufin ba za a koma shekarun 1980 ba, wanda a lokacin Philippines ta karɓi baƙuncin sojojin Amurka 15,000 inda aka jibge su a sansanoni biyu na Amurka mafi girma a nahiyar Asia.
A shekarar 1991, gwamnatin Philippine ta yi kira a lokacin. Ƴan ƙasar sun hamɓarar da gwamnatin kama karya ta Ferdinand Marcos tare da tura tsoffin jagororin mulkin mallaka gida.
Haka kuma yaƙin Vietnam yaƙi ne wanda aka daɗe ana yi, sa’annan yaƙin cacar baka kuma yana kawo ƙarshe, kuma a lokacin China ba ta da ƙarfin soji.
A 1992, Amurkawa sun tafi gida ko uma akasarinsu sun tafi.
Wani abu mai muhimmanci a yanzu shi ne sojojin China kuma suna da ƙarfi, kuma suna ƙwanƙwasa ƙofar Philippines.
Philippines tana zaune tana kallo amma babu yadda ta iya, inda har China ta sake fasalin taswirar Kudancin Tekun China ko kuma Yammacin Philippine kamar yadda ƙasar ke ambatar wurin.