Amurka Ta Aika Wa ‘Yan Najeriya Da Sako Na Musamman Akan Zabe Mai GabatowaABUJA, NIGERIA – Ta fadi hakan ne a cikin wani muhimmin sako na musamman da Amurka ta aike wa ‘yan Najeriya da safiyar yau.

Zabe ginshiki ne na yanci, ‘yan Najeriya kuma sun yi sa’a suna kasar da za su yanke hukuncin su kan wadanda za su jagorance su, amma hakan zai kasance ne idan su da kansu sun yi abin da ya dace, na shiga cikin shirin a dama dasu.

Saboda haka Amurka ke kira ga dukkannin ‘yan kasar dake da katin zabe dasu fito kwansu da kwarkwatansu don kada kuri’unsu a zabukan da za a yi cikin watannin Fabrairu da Maris.

Amurka Ta Aiki Wa ‘Yan Najeriya Da Sako Na Musamman Akan Zabe Mai Gabatowa

Amurka Ta Aiki Wa ‘Yan Najeriya Da Sako Na Musamman Akan Zabe Mai Gabatowa

Tun dai shekarar 1991 Najeriya keta hankoron samun yin zabe cikin lumana mai cike da adalci, Jakadiyar Amurka a Najeriya, uwargida Mary Beth Leonards, ta ce tun kama aiki da tayi yau shekaru uku a Najeriya kenan, ta ga gagarumin canje-canje da ka iya sa zabin jama’a ya yi tasiri a sha’anin zabe, musamman ganin a shekarar da ta gabata shugaba Buhari ya sanya hannu a sabuwar dokar zabe.

Amurka ta ce dokar zabe ta shekarar 2022 ba tantama ta karfafa tsarin zaben wanda wannan abin a yaba ne, musamman ganin yanzu hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar wato INEC za ta yi amfani da na’urar BVAS wajen tantance masu zabe, sannan a tura sakamakon zaben ta na’ura, al’amarin da Amurkan ta ce zai rage cuwa-cuwa da magudin zabe.

Amurkar, kazalika, ta kuma yi na’am da sabbin dokokin da zasu saukakawa masu nakasa yadda suma zasu kada kuri’unsu wanda hakan wani muhimmin mataki ne na tabbatar da an baiwa kowa da kowa damar kada kuri’a.

Wadannan kadan ne daga cikin ababen da ya sa Amurka keda kwarin gwiwa cewa hukumar zaben Najeriya zata aiwatar da zaben gaskiya mai cike da adalci.

Amurka kuma tayi na’am da aikin kwamitin zaman lafiya, abin dake zama wani ginshikin ganin an samar da kyakkyawan yanayin gudanar da zaben cikin lumana, musamman da yake jam’iyyu goma sha takwas da suka shiga zaben shugaban kasa sun amince zasu yi abin da ya dace don kauce wa rikici.

Sannan sunyi alkawarin karbar sakamakon zaben da zuciya daya kamar yadda hukumar INEC zata sanar.

AMURKA ZA TA DAU MATAKI KAN WADANDA SUKA YI WA ZABE ZAGON KASA:

A wani matakin ganin an yi zabe na fisabilillahi mai adalci, gwamnatin Amurka ta jaddada cewa zata dau matakin ladabtarwa ciki harda na kakaba takunkumin hana takardun VISA na shiga kasarta ga duk wadanda suka kuskura suka yi wa harkokin zaben zagon kasa, ta ma kowacce irin fuska kamar yadda ta yi a baya.

Samar da zabe cikin yanayin kwanciyar hankali mai adalci inji Amurka ba wai alhaki ne da ya rataya a wuyan ‘yan siyasa da kungiyoyi masu zaman kansu kawai ba, dole ne ‘yan Najeriya su tuna cewa su da suke da karfin ikon zaben shugabanni, to abune da ya kyautu ayi shi cikin lumana, sannan wadannan matakai ne ya kamata masu zabe su bi wajen ganin an tabbatar da zaben cikin nasara;

(1) Mai zabe ya je rumfar zabe da katin zabensa

(2) Mai zabe ya san rumfar zabensa kafin ma ranar zaben, a kuma duba karin bayani cikin yanar gizo na hukumar zaben

(3) Mai zabe yasan manufofin dan takara kan abin da ya ke ci mai tuwo a kwarya

(4) Ranar zabe mutum ya zabi dan takara don ya gamsu da shi zai kawo mai ci gaba.

A KUMA SAN WANNAN:

  • Muhimmin abin da ya kamata a sani shine sakamakon zabe abin dogaro,
  • Shi ne wanda hukumar zabe ta ayyana a hukumance bayan kammala tattara sakamakon zaben.
  • Kuma a sani cewa sakamakon zabe na zuwa da abubuwan ban mamaki kuma babu wani zabe da za ace ga takamaimai abin da zai faru

MATSAYIN GWAMNATIN AMURKA:

Amurka ta jaddada cewa bata da wani ‘dan takara da take goyon baya , babban muradinta shi ne gudanar da zabe na gaskiya mai cike da adalci da ya nuna zunzurutun abin da ‘yan Najeriya ke so.

Amurka na tunatar da ‘yan Najeriya cewa shiga a dama da mutum wajen hada hadar zabe a kasar wata babbar dama ce da miliyoyin mutane ke hankoron samu a kasashen duniya da dama amma basu samu ba, saboda haka koma wace jam’iyya mutum ke goyon baya, Amurka na shawartar ‘yan Najeriya da su fita su kada kuri’a ranar zabe, ta haka ne kadai za a yi alfahari da kasar a matsayin ginshiki a tsarin demokradiyya

KARSHE:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like