Rundunar sojin Amurka ta amsa cewa a karkashin abin da take kira kawancen yaki da ta’addanci da take jagoranta, ta kashe fararen hula 54 a Iraki da Syria a daga ranar 31 ga watan Maris na wannan shekara zuwa 22 ga watan Oktoba.
Tashar talabijin ta PressTV ta bayar da rahoton cewa, bisa ga wannan rahoto da Amurka ta fitar, a rana daya a cikin watan Yuli jiragen yakin Amurka karkashina bin da ake kira kawancen yaki da ta ta’addanci, sun kashe fararen hula 24 a yankin Minbaj da ke kasar Syria, yayin da rahoton ya ce a cikin shekaru 2, wannan kawance ya kashe fararen hula 170 a Iraki da Syria.
Sai a nasu bangaren kungiyoyin farar hula masu zaman kansu gami da na gwamnatocin Iraki da Syria, sun tabbatar da cewa adadin fararen hula da kawance Amurka ya kashe ya haura hakan nesa ba kusa ba.
Tun bayan kafa wannan kawance dai gwamnatin Syria ta nuna shakku matuka kan ingancinsa, domin kuwa kasashen da suka kafa kungiyoyin ‘yan ta’addan kuma suke daukar nauyinsu da makamai da kudade da da basu horon soji, su ne kan gaba a cikin kawance, da hakan ya hada da ita kanta Amurka, gami da Birtaniya, faransa da kuma Saudiyyah da Qatar.